Me ka ke nema?


Shafin Farko

Bulog


Gabatarwa

Bulog, wanda ake rubuta shi da blog a Turance, taƙaitawa ce ta kalmar Turanci ta weblog, wanda kuma nau’i ne na shafin Intanet da masana kamar irin su Dakta Oliver (2016), suka jefa shi cikin jerin shafukan sada zumunta. Shafi ne da ake tsara bayanan da ya ƙunsa a jere bisa tsarin sabon bayani a saman wanda ya gabace shi; wato abin da a Turance ake cewa reverse chronological order. Ana yawan sabunta bayanan da ke cikinsa; akan samu waɗanda ake iya sabunta bayanan da suka ƙunsa a duk kusan bayan awa guda ko kuma ƙasa da haka.

Wasu daga cikin irin waɗannan shafuka sukan mayar da hankali wajen rubuce-rubuce a kan darasi guda, wasu kuma, duk gurin da ta faɗi sha ne. Wasu daga ciki sukan zama shafukan jaridu, mujallu, makarantu wasu kuma na koyi-da-kanka kamar Taskira asirin mai ɗaki ga misali.

Shafukan Bulog, suna matuƙar bayar da gudunmawa wajen yaɗa manufofin da suka shafi siyasa, addini, ilimi, tallata haja, tattaunawa, harkokin cinikayya, kiwon lafiya da sauransu, ta yadda suke kasancewa hanyar kawo maƙudan kuɗaɗen shiga.

Wannan harka ta Bulog ta zama ruwan dare game duniya tare kuma da yin matuƙar tasiri da kaka gida a harkar sadarwar Intanet. Tasirinta ya kai har ga ta iya bayar da gudunmawar da ta kai ga ɗiɗe Trent Lott daga kujerarsa ta shugabancin masu rinjaye a Majalisar Dokokin Amurka a cikin shekarar 2002, sakamakon yayatawa tare kuma da kwarmata jawabin da ya yi game da yaƙin neman zaɓen kujerar shugabancin ƙasa na Strom Thurmond na shekarar 1948, kamar yadda McKenna da Pole (2007) suka ruwaito.

Wannan rubutu da ka ke karantawa, bayani ne game da Bulog, menene shi, irin moriyar da za a ci daga gare shi da ma yadda mai karatu zai ƙera nasa Bulog ɗin da sauransu.

Ma’anar Bulog

Masana sun bai wa wannan fasaha ta Bulog ma’anoni da dama, daga ciki akwai cewa: “Suna ne na shafin Intanet wanda ke nuna rubuce-rubucen (Postings) ɗaiɗaikun mutane ko sama da haka a jere bisa tsarin sabo a saman wanda ya gabace shi (Reverse chronological order) wanda kuma a mafiya yawan lokuta yake da majonin da yake bayar da damar yin tsokaci”, The Free Dictionary, (2019).

Weblog, wanda wasu lokutan ake rubuta shi da web log ko kuma Weblog, shafin Intanet ne wanda ke ƙunshe da bayanai da ake jera su bisa tsarin sabo a saman wanda ya gabace shi (Reverse chronological order), wanda kusan ake sabunta bayanan akai-akai (Rouse, 2019).

Daga waɗannan ma’anoni da muka kawo a sama, za mu fahimci cewa, shi bulog, shafin Intenet ne wanda yake ɗauke da bayanai da ake jera su a tsare, daga sama zuwa ƙasa tare da ɗora mafi sabunta a ƙololuwar sama.

Siffofin Bulog

Bulog, yana da wasu siffofi da suka bambanta shi da sauran shafukan Intanet. Daga ciki akwai:

  1. Ana tsara bayanan da ya ƙunsa a bisa tsarin ɗora bayani mafi sabunta daga farko ta sama zuwa ƙasa, abin da a Turance ake kira reverse chronological order.  
  2. Mafiya yawancin lokuta, bayanan da aka saka a bulog suna ɗauke da kwanan wata da kuma lokacin da aka shigar da su.
  3. Sunan marubuci yakan fita tare da lokacin da aka yi rubutun a mafiya yawancin lokuta.
  4. Akan adana tsofaffin rubuce-rubucen da suka gabata daki-daki, bisa tsarin watanni ko kuma shekara-shekara.
  5. Marubuta da makaranta sukan samu damar yin tsokaci game da rubutu a mafiya yawancin lokuta.
  6. Ana adana bayanan da ke cikin bulog rukuni-rukuni masu dangantaka da juna. Misali, za a iya adana dukkan bayanan da suka shafi harshen Hausa a ƙarƙashin Hausa, da sauransu.

Amfanin Bulog

Haƙiƙa, bulog, yana da matuƙar tasiri a rayuwar wannan zamani, kusan babu wani fanni na rayuwa da bulog baya bayar da gudunmawa kamawa tun daga kan nisaɗantarwa, ilimantarwa, wayar da kai da sauransu har zuwa kan samar da kuɗaɗen shiga. Saboda haka ƙididdige amfanin bulog a yau abu ne mai wahala, amma ga wasu kaɗan daga ciki:

  1. Samun kuɗaɗen shiga: Bulog, kafa ce da take mayar da mutane da dama hamshaƙan attajirai, ta hanyar tallace-tallace da suke samu. Babban abin nema shi ne ya zama mutum yana iya samun maziyarta.
  2. Tallata Haja: Bulog, kafa ce da masu sana’o’i za su baje kolin hajojinsu domin masaya su gani, su saya.
  3. Cinikayya: Bulog, kafa ce da yake taimakawa harkar cinikayya, ta yadda mai sayarwa zai je ya kasa kayansa, mai saye kuma ya gani ya saya ta hanyar latsa leɓen mawus ɗin kwamfutarsa ko kuma dangwalar fuskar wayarsa ko waninta. Kenan, ana iya buɗe shafin bulog da yake a matsayin kanti.
  4. Yaɗa Labarai: Bulog, kafa ce ta yaɗa labarai, akwai shafukan bulog barkatai a Intanet da suke a matsayin jaridu, mujallu, gidajen radiyo, talabijin da sauransu waɗanda suke bayar da dama wajen yaɗa labarai cikin sauri da kuma sauƙi.
  5. Samar da Guraben Ayyukan yi: Bulog, kyakkyawar kafa ce ta samar da ayyukan yi ga dukkan rukunin mutane, yana bayar da cikakkiyar damar da har daga cikingidaje da kuma ofisoshi ana iya tafiyar da su ba kuma tare da sun bayar da tasgaro ga aikin ofis ɗin ba.
  6. Yaɗa ilimi: Bulog, kafa ce mai matuƙar sauƙi da za a iya amfani da ita wajen yaɗa ilimi ta hanyoyi da dama. Malaman makaranta za su iya ɗura darrusan da suke karantarwa a aji domin ɗalibai su riƙa shiga suna karantawa.
  7. Faɗaɗa darasi: Bulog, dama ce da malami zai yi amfai da ita wajen faɗaɗa darasin da ya karantar a aji. Asali, idan darasi an ware masa awa ɗaya domin a karantar da ɗalibai wannan darasin, to ta hanyar bulog za a iya faɗa lokacin wannan darasin zuwa awanni marasa adadi. A nan malami zai ɗura darasin a bulog ɗalibai su riƙa shiga suna karantawa tare kuma da yin tambaya.
  8. Zai taimakawa ɗalibai wajen samun ƙarin haske a kan wani darasi bayan sun bar aji.
  9. Bayar da damar karatu ga ɗalibai daidai da fahimtar su, wannan kuma saboda ɗalibi yana da cikakken lokacin da zai bibiyi darasi sannu a hankali gwargwadon fahimtarsa.
  10. Bai wa ɗalibai damar gudanar da tattaunawa a tsakaninsu; wato abin da a Turance ake kira “Group Discussion”. Abin nufi shi ne cewa ɗaliban da suke karatu tare bayan an tashi daga makaranta, za su iya buɗe bulog su kuma taƙaita mahalarta darasin da iya yawansu. Misali, idan wasu abokai biyar suka haɗa kan su suna yi wa juna bita bayan an tahsi daga makaranta, za su iya buɗe bulog domin su riƙa tambayar juna suna kuma bai wa juna amsa.
  11. Yana ɗebewa ɗalibai kewar rashin kusantar abokan karatunsu.
  12. Ƙarfafar ɗalibai wajen fahimtar karatu.
  13. Haɗa abota/ƙwance tsakanin ɗalibai masu mabambantan harsuna, jinsi, rukunin shekaru, launukan fata da kuma kuma guraren zama.
  14. Za a iya amfani da bulog wajen neman bayanai domin gudanar da bincike a wani fannin na musamman.

Tasgaro

Babban tasgaro da bulog ya shahara da shi, shi ne bayar da damar yaɗa labaran ƙarya da kuma karkatar da mutane da sahihin ilimi; yin rubutu kan abin da mutum bai sani ba. Wannan kuma matsala ce da kusan a zamnatakewar yau-da-kullum ma ana fuskantar ta.

Rabe-Rabe

Akwai nau’ukan bulog da dama, kasantuwar ana iya rarraba ko karkasa su ta fuskoki da dama: bisa la’akari da yadda ake yin su; da kuma ta hanyar lura da abubuwan da suka ƙunsa. A wannan rubutun, siffa ta biyun za mu bi, kuma, za mu taƙaitu da waɗanda za mu kawo a ƙasa:

  1. Na Ƙashin Kai: Shi ne personal blog a Turance, bulog ne marabucinsa yake yin rubutu a kan duk abin da ya shafe shi kai tsaye kamawa daga tafiye-tafiyen da yake yi, harkokin siyasa, wasannin motsa jikin da yake yi, abubuwan da suke burge shi da waɗanda ya fi so da sauran abubuwan da suka shafi rayuwar marubucin kai tsaye. Shi irin wannan bulog ɗin ba shi alƙiblar rubutun da ta wuce bayar da bayani game da marubucin.
  2. Shaguna: Su ne bulog ɗin da suke tallata hajjojin masu su. Shafukan bulog ne da ake jera hotunan kayayyaki kowane da farashin su kamar a kanti.
  3. Gidajen Abinci: Shafu kan bulog ne da ake jera abinci iri-iri kowane da farashinsa.
  4. Na Sadarwa: Bulog ne da suke a matsayin jaridu, mujallau, gidajen radiyo, gidajen talabijin da sauran kafofin yaɗa labarai. A irin waɗannan bulog labarai kawai ake karantawa ko kuma sauraron sauti ko bidiyo a guraren da suka dace.
  5. Makarantu: Su kuma bulog ne da ke a matsayin shafukan darrusa wand aka iya kasancewa kai tsaye kamar ana aji ko kuma ana tattaunawa da abokin karatu domin samun ƙarin haske a kan wata gaɓa ta karatu.

Abubuwan Lura Wajen Buɗe Bulog

Akwai wasu muhimman abubuwa da ya kamata a sani kafin fara shiga harkar bulog matuƙar dai ana son kai wa gaci. Kaɗan daga ciki su ne:

  1. Manufa: Tushe ko ginshiƙin gina kowane bulog shi ne manufar samar da bulog ɗi. A wannan gaɓar, mai son gina bulog dole ya samu manufar da ta saka shi yake son buɗe wannan shafi na bulog, wadda kuma za a iya kallonta ta fuskoki da dama, daga ciki akwai neman kuɗi, yaɗa ilimi, manufar siyasa da sauran su.
  2. Makaranta: Abin nufi da makaranta a nan shi ne mutanen da ake so a kai gare su. Dole mai gina shafin bulog ya zama yana da wasu rukunin mutanen da yake son kai wag are su waɗanda ka iya zama malamai, ɗalibai, ‘yan siyasa, sarakuna, da sauransu.
  3. Ƙumshiya: Ƙumshiya a nan na nufin abu ko abubuwan da shafin zai ƙunsa. Dole ya zama bayanan da shafin zai ƙunsa sun yi daidai da manufar da ake son cimmawa. Idan kana nufin samun kuɗi da shafinka, to dole ka tsaya ka bincika ka gano abin da jama’ar da ka ke son yi wa rubutun suke da buƙata.
  4. Suna: Samawa shafi kyakkyawan suna mai bayyana kansa da kansa yana da matuƙar tasiri a harkar bulog. A nan ma ana so a samu daidaito tsakanin suna da kuma abin da shafin zai ƙunsa. Wato kar ya zama sunan daban, sannan kuma abin da shafin zai ƙunsa daban, wannan yana matuƙar korar masu ziyara.
  5. Rubutu: Yin rubutu a cikin sassauƙar siga tare kuma da kiyaye ƙa’idojin rubutu zai bayar da gagarumar gudunmawa wajen sauƙaƙa fahimtar abin da ake magana a kansa.
  6. Harshe: Zaɓin harshe, da ma’ana ta harshen da za a yi rubutun da shi, abu ne mai muhimmanci. A wannan gaɓar ma, ana so a samu daidaito tsakaninta da gaɓa ta biyu; wato ya zama an yi rubutun da harshen da masu karatu za su iya karantawa su fahimta cikin sauƙi. Ala misali, a ce Hausa.
  7. Kwalliya: Abin da nake nufi da kwalliya a nan shi ne design. Gina shafin bulog ƙayatacce mai cike da abubuwan ɗaukar hankalin masu karatu yana da amfani, saboda zai ƙara ɗebe wa masu karatu kewa su daɗe a shafin ba tare da ƙosawa ba.
  8. Haƙuri: Masu iya magana sun faɗa a cikin wata karin magana cewa; “Haƙuri wadar mai shi”, “Sannu-Sannu ba ta hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba”. Dole mai harkar bulog ya kasance mai haƙuri da duk irin abubuwan da zai ci karo da su a kan wannan hanya tasa.
  9. Naci: Dole mai bulog ya nace wajen yin rubuce-rubuce.
  10.  Sabunta Shafi: Yawan sabunta shafi yana jawo hankalin masu ziyartar shafi. Saboda haka, dole marubucin bulog ya nace tare kuma da haƙuri wajen yawan sabuta shafi da kuma yaɗa shi.

Madalla! Ya zuwa wannan gaɓar, ina kyautata zaton cewa ka ɗan samu ƙarin haske game da bulog, idan kana da sha’awa, sai ka latsa nan domin ka buɗe naka bulog ɗin.

Mazarta:


McKenna L. & Pole A. (2007). What do bloggers do: an average day on an average political blog. Ramapo College of New Jersey, Mahwah, NJ, USA; Brown University, Providence, RI, USA. Springer Science+Business Media, BV 2007

Oliver, K. H., (2016). Teaching with Blogs. Vanderbilt University Center for Teaching. An ciro a shekarar 2019, daga shafin: https://cft.vanderbilt.edu/teaching-with-blogs/ Read-Write-Thing (2008).

Common Blog Features. An ciro daga shafin: http://www.readwritethink.org/files/resources/lesson_images/lesson1113/ features.pdf, a shekarar 2019.

Rouse M. (2019). Weblog. An ciro a shekarar 2019, daga shafin www.whatis.com

St. John Fisher College (2008).What is a blog? An ciro daga shafin: http://citadel.sjfc.edu/students/anp03684/eport/msti%20331/What %20is%20a%20blog.pdf a shekarar 2019.

Wikipedia (2019). Blog. An ciro daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Blog, a shekarar 2019

WP Begginer (2019). Revealed: Which are the Most Popular Types of Blogs? An ciro daga shafin: https://www.wpbeginner.com/beginners-guide/which-are-the-most-popular-types-of-blogs/ a shekarar 2019


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub